Kafafen yada labarai sun hana gwamnatin Buhari sakat – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya bayyana cewa kafafen yada labarai sun taso gwamnati a gaba, sun hana ta sakat, har manyan jami’an ta ba su iya runtsawa su yi barci mai nauyi.

Lai ya yi wannan jawabi ne a yau Alhamis lokacin da ya karbi bakuncin ziyarar shugabannin Cibiyar Yada Labarai ta Kasa-da-kasa a ofishin sa a Abuja.

Ya ce kafafen yada labarai su daina wani shakku ko tsoron cewa wannan gwamnati za ta tauye musu ‘yancin albarkacin bakin su.

Maimakon, haka Lai ya ce, gwamnatin ce ma ke dari-dari da kafafen yada labarai domin sun taso ta a gaba da suka da caccaka.

Sai dai kuma yace ita gwamnati a koda yaushe ta na maraba da suka ko fadar ra’ayi mai ma’ana.

Daga nan sai ya yi roko ga kafafen yada labarai da su rika sara su na duban bakin gatarin su, ta hanyar suka mai fa’ida ba mai kunshe da son rai ba.

“A kullum mu na shan naushi da kutufo daga kafafen yada labarai. Ba cewa mu ka yi kada ka kushe ko a soke mu ba, amma dai kafin mai rubutu a kafafen yada labarai ya ragargaje mu, to ya tsaya ya natsu ya san abin da zai rubuta tukunna, kuma ya yi mana adalci. Ka na kuma ya yi la’akari da duba da irin matsalolin da gwamnatin nan ta gada.

Ya ci gaba da cewa tulin matsalolin da gwamnatin baya ta shafe shekaru 16 ta na laftawa kan Najeriya, ba za a iya magance su a cikin shekaru biyu ko shekaru biyu da rabi ba.

Idan ba a manta ba dai, jam’iyyar APC ta yi amfani da kafafen yada labarai ne wajen yin galaba kan PDP a lokutan kamfen na zaben 2019.

Share.

game da Author