KADUNA: Gwamnati ta ware miliyoyin kudi domin horas da malaman Sakandare

0

Kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha na jihar Kaduna Ja’afaru Sani ya bayyana cewa gwamnati ta ware Naira miliya 377 don horar da malaman makarantun sakandare a jihar wannan shekara.

Ya fadi haka ne da ya kai ziayara gani wa ido aikin da ake yi a kwalejin mata ‘Government Girls College’ dake Zonkwa yau Alhamis, sannan ya kara da cewa gwamnati ta tsara horon ne saboda da ta samar wa malaman makarantun jihar dandali da zasu kara karatu kan abin da suka sani da ma wanda basu sani ba.

Daga karshe ya ce za su yi wa yan kwangilan gyara makarantar su hanzarta kammala aiki da sue yi domin dalibai su dao karatu.

Share.

game da Author