KADUNA: Gwamnati ta wadata asibitoci da maganin Amai da Gudawa

0

Shugaban fannin hana yaduwar cutuka na karamar hukumar Jema’a jihar Kaduna Abdullmumin Bala ya bayyana cewa sanadiyyar bullowar mutane biyu sun rasa rayukan su a yankin sannan wasu 82 na kwance a asibiti a kafanchan.

Bala wanda ya sanar da haka wa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kafanchan ranar Litini ya ce cutar ta fara bullowa ne a Kafanchan da kuma kauyukan Katsit, Takau da Katsak.

Ya ce yara kanana ‘yan shekaru 1 zuwa 5 ne suka fi kamuwa da cutar sannan suna samun kulan da suke bukata a asbibiti.

Bala ya kara da cewa fannin kiwon lafiya na karamar hukumar Jema’a ta kirkiro wasu hanyoyi domin wayar da kan mutane hanyoyin da zasu bi don gujewa kamuwa da cutar da hana yaduwarta.

Darektan fannin kiwon lafiya na karamar hukumar Sarah Dadai ta ce asibitin Kafanchan ta sallami yara 82 wanda suka kamu da cutar sannan ta ce tare da hadin gwiwar ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Kaduna karamar hukumar Jema’a ta sami nasaran dakile yaduwar cutar.

Daga karshe ta ce ma’aikatar ta kuma samar wa asibitocin da yara 82 suka kwanta da magungunan cutar amai da gudawa domin hana yaduwar cutar nan gaba.

Share.

game da Author