Kada Buhari ya kuskura ya ce zai sake takara, ya hakura hakanan, Inji Babangida

0

Mako daya bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hakura da mulki bayan ya kammala zangon sa na farko a 2019, shima Ibrahim Babangida wanda tsohon shugaban Najeriya ne ya yi kira ga Buhari da ya hakura da mulki bayan 2019.

Babangida ya bayyana haka ne a wata doguwar wasika da ya rubuta wa shugaba Muhammadu Buhari in da ya yi kira gare sa da ya hakura bayan ya kammala zangon sa na farko a 2019 ya koma ya huta.

Babangida ya ce Najeriya na bukatan sabbin jini ne yanzu ba tsuffi ba.

” Kasar nan da tsintsiya ce madaurinta daya amma yanzu abin duk ya wargaje. A wannan gwamnati an maida jinin mutane ba komai bane. Ko-ina yanzu kisa akeyi, jinin mutane na kwarara kamar teku.

” A Zamfara an kashe mutane sama da 200, yankin kudancin Kaduna, Jihar Ribas da Taraba duk abin ba a cewa komai. Yanzu Najeriya ta zama kasa da kwararar jini bai zama komai ba.

” Dole ne mu hada kai mu taimakawa Buhari ya kammala wannan zango ta sa, bayan haka a 2019 sai kuma a samu wani sabon jini  ya zo ya karbi mulkin. Domin samun ci gaban da ya kamata musamman a wannan lokaci da duniya ya ci gaba.Yanzu batun ci gaban kimiyya a keyi ba irin abin da aka sani a da ba.

Babangida ya kalubalanci shirin wannan gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa inda ya ce gwamnatin nan ta kasa gano bakin zaren. Yadda ta ke fatattakar barayin gwamnati da sunan yaki da cin hanci da rashawa ba haka ne ya kamata ace wai an bi wannan matsala ba.

” Ba fatattakar bane matsalar, gano bakin zaren ne har yanzu wannan gwamnati ba ta iya yi ba. Idan ba gano bakin zaren tayi ba babu ta inda za a iya kawo karshen wannan matsala na cin hanci da rashawa, wanda shine tottoshe kafar da za a oya samun baraka kamar haka sannan abi ana dakile hanyoyin da akanyi amfani da su wajen wawuran kudaden gwamnati.

” Canjin da aka yi ta tallatawa cewa shine lakanin wannan gwamnati bai yi wa kasa amfanin komai ba. Ni na dauka ai gwamnatin canji zai kawo sauye-sauye ne da zai karkatar da salon mulkin daga yadda aka saba, akawo wasu canje-canje da zai canza salon mulki a Najeriya, sai ga shi maimakon haka ci baya ma aka samu. Yadda dai aka saba shine aka ci gaba da yi.

Babangida ya kara da cewa dole akawo sauyi a yadda fasalin jami’an tsaron kasar nan yake da ya hada da na ‘yan sanda da na Soji.

” An ci gaba a duniya, saboda haka dole ne Najeriya ita ma ta ci gaba. A canza salon samar da tsaro a kasar nan.

Bayan wasu ababe masu dama da ya yi tsokaci a kai kiran sa daga karshe shine, Buhari ya hakura hakanan bayan ya kammala zangon sa na farko, a nemi sabon jini su ci gaba da Jan ragamar mulkin Najeriya ko ta iya bugun kirji da kasashen duniya da suka ci gaba.

Share.

game da Author