Kada Buhari ya bi shawarar Obasanjo – Oshimhole

0

Tsohon Gamnan jihar Edo, Adams Oshimhole ya bayyana cewa kada ma Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya ya saurari shawarar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ba shi cewa kada ya nemi zango na biyu.

Oshimhole wanda ya amsa tambayoyi bayan ganawar da ya yi da shugaban kasa. Tun da farko ya bayyana cewa ya je gaisuwa fadar ce saboda rabon shi da ciki tun 2017, kuma yanzu an kusa kada gangar siyasa.

Ya ce don haka a matsayin sa na dan APC, ya je ne ya kara jaddada mubayi’ar sa ga Buhari kan zaben 2019. Tsohon gwamnan ya ce maganar Obasanjo ba abin kamawa a rike ba ce.

Ya tuna cewa, “Ba zan manta ba lokacin da Obasanjo ke kan mulki, da ya nada masu ba shi shawara, sai ya ce aikin su shi ne ba shi shawara, amma fa shi ma ya na da nasa ra’ayin na kansa.”

Da aka yi masa batun fatara da talauci da ake fama da shi, sai ya ce, “wato an dade ana maganar fatara tun ya na shugabancin kungiyar kwadago ta kasa, NLC ake yin fafutikar.

” Wato idan ku ka duba abin da ke bambamta kasashen Afrika da wadanda su ka ci gaba, shi ne mummunan cin hanci, rashawa da wawaure kudade ne ya hana mu ci gaba har su ka yi masa rata mai tazara sosai.

Sai Adams ya ce muddun ba a matsa an gyara matsala rubdugu ba, to za a yi ta tsalle a wuri daya ne, ba ma za a iya magance sauran matsalolin ba.

Sai ya yi tsinkayen cewa amma a yanzu Shugaban Kasa ya kamo bakin zaren matsalar almubazzaranci da rashawa. Kuma ya yi nunin cewa ya kamata a yi la’akarin irin gagarimar barnar da gwamnatin Muhammadu Buhari ta taras an tabka.

Share.

game da Author