Jihar Neja za ta fara raba wa manoma takin zamani daga watan Maris

0

Kwamishinan aiyukkan noma da ci gaban yankunan karkara na jihar Neja Nuhu Dukku ya bayyana cewa gwamnati za ta fara rabawa manoma takin zamani daga watan Maris zuwa Afrilun 2018.

Ya sanar da haka ne a hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Minna.

Dukku ya ce gwamnati ta ce za ta hada hannu da wani kamfanin sarrafa takin zamani domin samar da takin da wuri wa manoman jihar.

” Bana dai gwamanti baza ta jira har sai gwamnatin tarayya ta wadata jihar da taki ba za mu samar wa manoman mu da taki cikin lokacin da ya kamata.”

Share.

game da Author