Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta dakatar da Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa Sanata Suleiman Hunkuyi daga jam’iyyar.
Da yake sanar da haka wa manema Labarai a Kaduna, sakataren jam’iyyar Yahaya Baba Pate ya ce jam’iyyar ta yanke wannan shawara ne don hukunta Sanata Hunkuyi kan laifin kirkiro wata bangaren jam’iyyar APC a Jihar a makon da ya gabata.
Hunkuyi ya gargadi gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da ya amsa wani korafi da akeyi masa cewa yana wa jam’iyyar a Kaduna zagon Kasa.
Sakatare Baba Pate ya Kara da cewa uwar jam’iyyar ta gargadi Sanata Hunkuyi da ya shiga taitayin sa duk da cewa ba zata iya korar sa ba a matsayin sa na Sanata ta dakatar dashi na tsawon watanni shida
daga jam’iyyar a Jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Barnabas Bantex, Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Aminu Shagali, na daga cikin wadanda suka halarci taron jam’iyyar a Kaduna.
Discussion about this post