Jami’an Kwastan na jihar Ohun sun kama kwalayen kwakwa 88 da kuma wasu kwalaye na littattafai 44 makare da taba wiwi a kan iyakar jihar da Jamhuriyar Benin.
Kakakin Yada Labarin Kwastan na Jihar Ogun, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana wa PREMIUM TIMES a jiya Lahadi.
Ya ce an damka kayan tabar wiwi din ga jami’an Hukumar Hana Fataucin Kwayoyi, NDLEA.
Maiwada y ace an samu nasarar damke tulin wiwi din bayan da wani ya tsegunta wa kwastan yadda ake kokarin safarar tabar.
Ya ce bayan an kama kayan, sai Shugaban Kwastan na Ogun, Sani Madugu ya umarci a damka su gaba daya ga Hukumar NDLEA.
Kakakin ya kuma nuna matukar damuwar sa kan yadda jama’a ke ta kokarin shigo da mugayen kwayoyi su na lalata al’umma.
Sannan ya ce za su ci gaba da kokarin ganin masu shigo da muggan kwayoyi ba su samun nasara a kasar nan.