INEC ta roki EFCC ta binciki inda Jam’iyyun siyasa ke samun kudin kamfen

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa, INEC, ta roki hukumar EFCC cewa ta rika bin diddigin hanyoyin da jam’iyyun siyasa ke samun kidaden da su ke kashewa da nufin tabbatar da ana bin ka’idar adadin kudaden da doka ta yanke a kashe a yayin kamfen.

Shugaban Hukumar ne, Mahmood Yakubu ya yi wannan kira a lokacin da Shugaban EFCC Ibrahim Magu ya kai masa ziyara a ofishin sa a jiya Alhamis.

Yakubu ya shaida wa Ibrahim Magu cewa ya zama tilas EFCC ta yi haka, domin kada a bari kudi su kasance abin da as a yi amfani da shi a ci zabe a 2019.

Dokar Zabe ta 2010 dai ta amince dan takarar shugaban kasa ya kashe naira bilyan daya (N1b).

An amince wa dan takarar gwamna us kashe naira milyan 200.

Shi kuma dan takarar sanata naira milyan 40 yayin da dan takarar majalisar tarayya zai kashe naira milyan 20 kadai.

Dokar kuma ta haramata wani mutum ko wata kungiya ya ba jam’iyya gudummawar kudin da su ka sama da naira bilyan daya.

Akwai hukunci mai tsakani ga dan takarar da ya karya doka.

Yakubu ya ce INEC ta damu da yadda ake fitowa da kudi muraran a wurin dangwala kuri’a aka sayen kuri’un jama’a.

“Bayan kammala zaben 2015, mun samu rahoton EFCC inda ta kama ma’aikatan INEC 205 da laifin harkalla.

“Amma fa banda wadannan baragurbin, INEC na da hazikan ma’aikata masu kishi. Dalili kenan ma mu ka kara wa 7335 daga cikin su matakai da matsayi kenan a cikin 2017.

Magu ya nuna jin dadin kiran da Yakubu ya yi masa, ya na mai cewa tun a baya EFCC ta sha binciken harkalloli da dama da su ka shafi laifukan zabe.

Ya sha alwashin yin aiki kafada-da-kafada da INEC domin a kara tsaftace zabe.

“Ba za mu yarda ‘yan sisaya na yanka wa dimokradiyya farashi su na sayen kuri’un jama’a ba.” Inji Yakubu.

Share.

game da Author