INEC da Hukumar Kidaya za su kakkabe sunayen matattu daga rajistar zabe

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta nemi hadin kan Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da ta bata sunayen wadanda su ka rasa rayukan su, daga 2015 zuwa yau, domin ta yi kakkaba da sharar sunayen wadanda suka mutu daga rajistar zabe.

Shugaban INEC, Farfesa Mahood Yakubu ne ya yi wannan kira a lokacin da ya kai wa Shugaban Hukumar Kidaya, Eze Durulheoma ziyara a ofishin sa a Abuja.

Ya ce ya zama dole ya INEC ta samu rakod na sunayen wadanda suka mutu domin ta hakan ne kawai za ta iya samun sunayen matattaun da za a cire na su sunayen daga cikin jerin masu rajista na kasar nan.

“Idan muka yi haka, INEC da Hukumar Kidaya za su yi aikin hadin guiwa kenan domin mu tantance sunayen masu rajistar wadanda suka mutu daga 2015 zuwa yau.

“Sannan kuma mu na da cikakken yakinin cewa za ku ba mu hadin kai kan wannan aikin tantancewa mai muhimmaci da ke gaban mu.

Yakubu ya ce INEC za ta yi dukkan kokarin da ya wajaba domin ta tabbabar da zaben 2019 ya yi nasara sosai kuma an gudanar da shi a bisa turbar adalci, kuma ya kasance sahihi, ba tare da tashin-tashina ba.

A nasa jawabin Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa, ya tabbatar da cewa hukumar sa za ta baiwa INEC hadin kai sosai.
Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba ma NPC din za ta fara aikin tattara bayanan wadanda su ka mutu a fadin kasar nan kuma da zaran ta kammala, za ta damka wa INEC.

Wannan aikin tantance wadanda suka mutu daga cikin rajistar INEC, ya zo ne a daidai lokacin da hukumar zaben ta bayyana cewa a yanzu haka akwai rajistar masu zabe a hannun hukumar har kimanin miliyan bakwai da har yanzu masu su ba su je sun karba ba.

Share.

game da Author