Kasim Afegbua, maitaimakawa tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida kan harkar yada labarai ya bayyana cewa yana nan akan bakan sa cewa wasikar da ya fitar daga tsohon shugaban kasa Ibarahim Babangida ta fito sannan da izinin sa ya saki wa ‘yan jarida.
Idan ba a manta jim kadan bayan an buga wasikar a kafafen yada labarai, tsohon shugaban kasa Babangida ya saki wata sabuwar wasika yana karyata waccen da kakakin sa ya fitar.
A wasikar sa ta farko, Babangida ya ce Najeriya na bukatan sabbin jini ne yanzu ba tsuffi ba. Yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hakura da mulki bayan ya kammala zangon sa na farko a 2019.
Babangida ya kalubalanci shirin wannan gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa inda ya ce gwamnatin nan ta kasa gano bakin zaren. Yadda ta ke fatattakar barayin gwamnati da sunan yaki da cin hanci da rashawa ba haka ne ya kamata ace wai an bi wannan matsala ba.
” Ba fatattakar bane matsalar, gano bakin zaren ne har yanzu wannan gwamnati ba ta iya yi ba. Idan ba gano bakin zaren tayi ba babu ta inda za a iya kawo karshen wannan matsala na cin hanci da rashawa.
Wanda shine tottoshe kafar da za a oya samun baraka kamar haka sannan abi ana dakile hanyoyin da akanyi amfani da su wajen wawuran kudaden gwamnati.
” Canjin da aka yi ta tallatawa cewa shine lakanin wannan gwamnati bai yi wa kasa amfanin komai ba. Ni na dauka ai gwamnatin canji zai kawo sauye-sauye ne da zai karkatar da salon mulkin daga yadda aka saba, akawo wasu canje-canje da zai canza salon mulki a Najeriya, sai ga shi maimakon haka ci baya ma aka samu. Yadda dai aka saba shine aka ci gaba da yi.
Sifeto-Janar din ‘yan sandan kasa Ibrahim Idris ya bada umurnin a kama Kasim, cewa ana zargin sa da laifi yin kazafi, da bata suna a wasikar da ya saki.
Kasim ya ce ya sanar wa lauyoyin sa, kuma suna nan suna duba bayanan ‘yan sandan, sai dai kuma ya fadi cewa yana nan kan bakan sa cewa IBB ne ya umurce shi ya saki wannan wasika.
” Zan kai kaina ofishin ‘yan sanda ranar Laraba, amma yanzu lauyoyina na duba bayanan ‘yan sandan. Kafinnan zamu san wace wainar za a soya.