Tsohon gwamnan jihar Neja Aliyu Babangida ya bayyana cewa ba zai canza sheka daga jami’yyar PDP zuwa daga jami’yyar PDP.
Ya sanar da haka ne wa manema labarai a garin Minna bayan wasu ‘yan Jami’iyyar PDP 34,826 da ya hada da mataimakin shugaban jami’iyyar PDP na jihar Aminu Yusuf sun koma APC.
Kamfani dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa mafi yawan mutanen da suka canza shekan zuwa APC aminan tsohon gwamna Aliyu ne.
” Duk da cewa jami’iyyar PDP na fama da wasu ‘yan matsaloli da yanzu haka muna kokarin ganin mun warware su, hakan ba zai sa in canza sheka ba, ina na tare da PDP don ko ita ce ta yi sanadiyyar zama na gwamna a 2015.
Discussion about this post