Idan rahoton El-Rufai ya iso Majalisa, za mu yi amfani dashi a ban daki, sauran kuma a raba wa masu sai da kosai – Sanata Sani

0

Sanata da ke wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa Shehu Sani ya bayyana cewa bai ga amfanin da rahoton sake fasalin kasa da Kwamitin da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya shugabanta da jam’iyyar APC ta kafa ba.

Idan ba a manta ba jam’iyyar APC ta kafa kwamiti domin duba yadda za a sake fasalin kasa Najeriya da irin shawarwari da zata bada wanda gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya jagoran ta.

Sanata Shehu Sani ya ce maganan sake fasalin kasa ba ya gaban majalisar kuma ba za a yi hakan ba yanzu, sannan ba za ayi ba ko bayan 2019.

Yace idan ma aka kawo musu wannan takardu tattara shi za suyi a rabawa sanatoci 109 da ke majalisar tarayya kowa ya je dashi ban daki sannan idan yayi saura kuma a raba wa masu soya kosai da masu gasa nama da suke sana’ar su a kewayen majalisar.

Sanata Sani ya zargi El-Rufai da yin fuska biyu ga batun sake fasalin kasa da aka tado.

” A da can El-Rufai ya nuna adawarsa karara kan wannan shiri, sai gashi yanzu ya lashe amansa.”Inji Shehu Sani.

Share.

game da Author