Hukumar NDE za ta horas da ‘yan gudun hijira 11,300 sana’o’in hannu a jihar Barno

0

Hukumar samar da aikin yi na kasa NDE mallakin ma’aikatar kwadago ta sanar da cewa za ta horas da ‘yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin kasar nan sana’o’in hannu.

Jami’in ma’aikatar Ibrahim Jibiya wanda ya wakilci Ministan kwadago Chris Ngige a taron fara wannan hidima da aka yi a Maiduguri a jiya Talata ya ce horas da ‘yan gudun hijira 11,300 da hukumar NDC za ta yi na daya daga cikin tsarin inganta rayuwar su da gwamnatin Buhari ke kokarin yi.

” A wannan tsarin za ta fi bada karfi wajen horas da mata ne.”

” Sana’o’in hannun da za a koyar sun hada da yin sabulu, hada turare, manshafawa, rini, gyaran kai da sauransu wa matan sannan sana’o’in hannu kamar su kanikanci, gini, kafinta, gyaran wayoyi kuma wa maza.”

” Sannan bayan an horas da su za mu basu kudade da kayan aiki domin fara sana’o’in su.”

Daga karshe mataimakin gwamnan jihar Barno ya jinjina wa gwamnatin Buhari saboda kawo wa yankinsu wadannan ci gaba.

Share.

game da Author