Hukumar NCAA ta fara binciken dalilin rikitowar murfin kofar jirgin Dana

0

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Kasa, NCAA, ta fara binciken musabbabin rikitowar murfin kofar jirgin sama na kamfanin Dana da aka ce ya rikito a jiya a daidai lokacin da jirgin ya diro kasa.

Kakakin Hukumar, Sam Adurogboye ya tabbatar da fara binciken kuma ya tabbatar da afkuwar rikitowar murfin kofar jirgin a ranar Laraba.

Sai dai kuma kamfanin Dana ya ce babu yadda za a yi murfin kofar ya rikito kasa, idan har ba daya daga cikin fasinjojin ko kuma matukan jirgin ne ya taba shi ba.

Kakakin kamfanin Dana Kingsley Ezenwa, ya ce za a gudanar da bincike domin a gano gaskiyar lamari.

Sai dai kuma wasu fasinjojin sun ce tun a kololuwar samaniya suka fara ganin murfin kofar na jijjiga kuma iska na shiga cikin jirgin. Su ka ce hakan ta sa kowa ya rarumi bel din sa ya daura tamau.

“Lokacin da jirgin ya dira kasa, sai mu ka ji wata irin kara mai firgitarwa. Ashe murfin kofar ce ya rikito kasa, sai ga mu hanhai hasken rana ya keto cikin jirgin.”

Fasinjojin sun karyata ikirari da jami’an Dana su ka yi cewa data daya cikin fasinjojin jirgin ne ya taba murfin kofar.

Tuni dai ake ta watsa wani bidiyo da daya daga cikin fasinjojin jirgin ya dauka, a lokacin da murfin kofar ya rikito kasa.

Share.

game da Author