HAJJIN BANA: Jihar Kogi ta koka kan karancin kujerun hajji

0

Hukumar Alhazai na jihar Kogi ta koka kan karancin kujerun zuwa hajji da aka bata a hajjin bana.

Bana jihar ta sami kujeru 717, bara ta sami 838 wanda idan aka kwatanta yawan su za a ga cewa yawan kujerun ba za su isa duka masu burin zuwa aikin hajji bana ba.

Shugaban hukumar Lukman Abdullah ne ya sanar da haka da ya kai wa shugaban kungiyar ma’aikatan jarida Momoh Jimoh ziyara a ofishin sa dake Lokoja.

Lukman ya kara da cewa hukumar na iya kokarin ta don ganin ta sami karin yawan kujerun musamman yanzu da suka fara shirye shiryen aikin hajjin.

Ya ce babbar matsalar da ke ci wa hukumar tuwa a kwarya shine rashin lokaci don maniyyata su iya kammala biyan kudaden tafiyar su.

” Don guje wa irin haka ne ya sa muka daga ranar daina karban kudaden maniyyata zuwa 31 ga watan Maris.”

Abdullah ya ce hukumar ta samar wa mahajjata wuraren zama kusa da masallacin Makka da Madinah sannan suna gab da kammala sauran shirye shiryen da zai hada da kula da walwalar mahajjata kafin su bar Najeriya, yayin da suke kasar Saudi da bayan sun dawo aikin hajjin.

Share.

game da Author