Jiya ne Karamar Ministar Harkokin Waje, Khadija Bukar Abba da Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa, Abdullahi Mohamme su ka gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari bayanin irin shirye-shiryen da Najeriya ta yi dangane da aikin Hajjin bana na 2018.
Shugaban Hukumar Alhazai ya bayyana cewa Saudiyya ta ware wa maniyyata dubu 95,000 daga Najeriya gurbin shiga kasar domin su gudanar da aikin Hajji.
Kamar yadda ya ci gaba da bayani, an ware dubu 70,000 ga Hukumar Alhazai, yayin da dubu 20,000 kuma aka ware wa kamfanonin hada-hada masu zaman kan su, wadanda aka fi sani da International, ko kuma jirgin-yawo.
Daga nan kuma ya ci gaba da cewa, sai dai kuma tun daga 1 Ga Janairu, 2018, kasar Saudiyya ta bayyana cewa daga yanzu ta dora haraji ‘VAT’ a kan kowane kayan da mahajjaci zai saya ko zai yi amfani da su a can, musamman kayan abinci da sauran ayyukan da kasar ke aiwatarwa domin Mahajjata.
Saudiyya ta kuma yi gargadin cewa a cikin watan Mayu za ta rufe kofar duk wasu shirye-shiryen aikin Hajji, don haka ya kamata Nijeriya da maniyyata su gaggauta shiryawa da wuri.
Shugaba Buhari ya yi musu alwashin cewa gwamnati za ta bayar da cikakken goyon baya wajen aiwatar da dukkan abin da ya wajaba ga maniyyata, musamman kulawa ta fannin laFiya, tsaro da kayan more rayuwa.