Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhazan jihar Kaduna, Yunusa Abdullahi, ya bayyana cewa jihar ta sami kujerun hajji 6,632.
Abdullahi da ya sanar da haka wa manema labarai a Kaduna ya kara da cewa yanzu haka maniyyata sama da 1000 sun fara biyan kudin hajjin su.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da karbar kudin maniyyata har zuwa watan Maris lokacin da za ta rufe rijistan maniyyata.
Ya kuma ce za a fara karantar da maniyyata hukunce-hukuncen hajji nan ba da dade wa ba.