Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya yi kira ga gwamnonin Arewa 19 su fito da wani tsari na bai-daya da zai iya magance rikicin makiyaya da manoma, wanda ya dade ya na haifar da asarar rayuka.
Masari ya yi wannan jawabi ne lokacin da sabon shugaban kungiyar ‘yan Jaridu ta Kasa, NUJ, na jihar Katsina, Abdulhamid Sabo ya kai masa ziyara.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne kwanaki kadan bayan da gwamnan jihar Kano ya gayyaci daukacin makiyayan da ke Arewa su yi kaura daga duk inda su ke su koma jihar Kano, domin akwai yalwar wurin kiwo a jihar.
Shi ma Masari ya ce gwamnoni na da dama da kuma hanyoyin magance wannan mummunar kashe-kashe da ake yawan yi a rikicin makiyaya da manoma.
Ya ce yankin Arewa na da fadin kasa da yalwar wuraren kiwo, maimakon makiyayan nan su rika gallafiri daga nan zuwa can ana haddasa kashe-kashe.
Ya ce su dawo yankin Arewa su zauna, sannan za a gina musu makarantu da sauran ababen more rayuwa kuma shanun su za su yi kiwo cikin walwala.