Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kasar nan, Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewa kyale kowace jiha ta kafa ‘yan sandan ta zai magance matsalar tsaro a fadin kasar nan.
Yari wanda shi ne gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana haka ne a karshen rufe taron kwana biyu da aka gudanar dangane da kalubalen da kasar nan ke fuskanta a fannin tsaro.
Ya ce “mu ma a yau mun goyi bayan matsayar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya amince da ita cewa ya goyi bayan kowace jiha ta kafa ‘yan sandan ta.”
“Dama kuma matsayar da mu ka cimma kenan a taron da mu ka yi cikin watan Agusta cewa akwai bukatar kafa ‘yan sandan jihohi.
“Maganar gaskiya ba za mu iya kula da kare dukiyoyi da rayukan kasar nan daga Abuja ba. Don haka akwai bukatar kafa ‘yan sandan jiha.”
Ya ce a misali, akwai kusan mutane miliyan hudu a jihar Zamfara, amma kuma jami’an ‘yan sandan da aka tura a jihar ba su fi 5,000 ba. “
Dangane tsadar yadda za a rika kashe kudin tafiyar da ‘yan sandan jihohi, Yari ya ce ai dama ba a ce kowace jiha sai ta kafa ba. Wadda ke bukata kuma ta na da karfin daukar nauyin su, ita ce jihar da za ta kafa.
Ya kara da cewa amma idan aka yi la’akari, za a ga fadace-fadace da Boko Haram, barayin shanu, rikicin Neja Delta da sauran rikice-rikice sun gurgunta tattalin arzikin kasar nan a cikin shekaru goma da suka gabata zuwa yau.
Discussion about this post