Kwamishinan aiyukkan kananan hukumomi da sarakunan gargajiya na jihar Zamfara Bello Dankande ya bayyana cewa gwamanti ta yi wa mutane 2,800 aiki a idanuwar su kyauta a wasu kananan hukumomi dake jihar.
Dankande ya tsokata wa manema labarai ne bayan ya gana da wadanda aka sallama a karo na farko cikin wadanda akayi wa aiki a asibitin King Fahad a Gusau.
Ya ce gwamnati ta yi haka ne tare da hadin guiwar kungiyar likitocin mai zaman kanta na ‘Visions Saver Eye Care Limited,’ inda aka zabo mutane 2,800 daga kananan hukumomin Gusau, Bungudu, Maru da Tsafe.
Ya ce wannan shiri zai yi wa mutane sama da 9000, kafin a kammala shi.
Daga karshe shugaban asibitin King Fahad, Bello Mafara yace bayan bada magani da aiki da likitocin ke yi a asibitin su kan wayar wa mutane kai game da yadda za su iya guje wa kamuwa da kowace irin cutar dake kama idanu.
Discussion about this post