Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa Jihohi da naira Tiriliyan 1.9 a shekarar 2017

0

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya sanar wa baki da ‘yan Kasa da suka halarci taron kirkiro da sake fasalin tattalin arzikin kasa da ka yi yau a garin Lokoja cewa, gwamnatin Buhari ta tallafawa jihohin kasar nan da Kudade har naira Tiriliyan 1.9 a shekarar da ta gabata.

Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne don ta agaza wa jihohin su gudanar da manyan aiyukan da suka sa a gaba.

Da ya ke nasa jawabin a wajen taron, gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya fara ne da rokon mabiya addinin kirista da su yafe masa wani cin fuska da yayi wa shugabannin su.

Ya roke su da su yi hakuri su yafe masa.

Bayan Gwamna Bello ya godewa Osinbajo sannan kuma yayi alkawarin canza salon yadda ake tafiyar da gwamnati a jihar cewa gwamnatin sa ta tsaro wasu shirye-shirye domin ganin jihar ta bunkasa musammam ta hanyar kirkiro da masana’antu da sauran su.

Share.

game da Author