Gwamnatin Sokoto za ta gina tituna da zasu kai tsawon kilomita 500 a fadin jihar

0

Gwamnatin jihar Sokoto tare da hadin guiwar Bankin Duniya za ta gina tituna a fadin jihar da ya kai tsawon kilomita 500.

Kwamishinan Kudin jihar, Saidu Umar ya bayyana cewa gwamnati za ta gina titunan ne a yankunan mazaubun sanata uku da ke jihar.

” Yanzu mun kammala shiri tsaf, muna jiran wakilan Bankin Duniya ne su zo mu kammala zabo hanyoyin da za ayi domin tunkarar su gadan gadan.” Inji Umar

Ya ce suna so suyi aiki ne wanda kowa ya gani zai yaba.

Share.

game da Author