Jakadar kasar Australia a Najeriya Paul Lehmann ya bayyana cewa kasar Australia za ta inganta rayuwar nakasassu 36,700 a Najeriya a wata hidama da za ta fara a shekarar 2020.
Lehmann wanda ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Legas yau Alhamis ya ce kungiyoyi masu zaman kansu daga kasar ne za su hadu domin samar da wannan tallafi.
Ya kuma ce wannan ba shine karo na farko da kasar za ta tallafa wa nakasassu a Najeriya ba. Ya ce kasar ta tallafawa yara makafi da na’urar ‘Computer’ a makarantar nakasassu dake jihar Enugu sannan ta kuma bude wurin kiwon kaji a makarantar nakasassu dake jihar Filato.
Ya kuma ce sun bube wajen koyar da sana’o’in hannu a makarantar nakasassu a Abuja.
Daga karshe Lehmann ya ce gwamnatin Autralia a shirye take domin kawo hidimomin da za su inganta rayuwar wadannan mutane a kasar nan daga nan har zuwa shekaru masu zuwa.