Gwamnatin tarayya ta samar da na’urorin gwajin cutar daji a asibitin kula da masu fama da cutar daji dake Abuja.
Shugaban asibitin Jeff Momoh da ya sanar da haka ya ce gwamnati ta yi haka ne domin bunkasa aiyukan asibitin ganin cewa na’urar da ake amfani da ita ta tsufa.
” Hakan da gwamnati ta yi zai kawo sauki ga matsalar rashin kayan aiki da ake fama dashi a kasar nan musammam wanda ya shafi cutar daji da kan sa dole sai anfita zuwa kasashen waje.
Momoh ya kuma kara da cewa gwamnati ta horas da wadanda za su dunga amfani da wannan na’ura yadda ya kamata domin tabbatar da inganci na’uran.
Daga karshe yace gwamnati za ta samar da irin wadannan na’urori a duk shiyoyin kasar nan domin kulawa da wadanda ke fama da wannan cutar.
Discussion about this post