Gwamnati ta ciyar daliban firamare abinci sama da miliyan 200

0

Ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati ta raba abinci sama da miliyan 246 a shirin ciyar da daliban firamare da ka fara a watan Disambar 2016 a jihohi 20.

Kakakin mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya sanar da haka inda ya kara da cewa yawan daliban zai iya karuwa zuwa dalibai 313 nan da watan Faburairu saboda wasu jihohin za su shiga shirin.

Akande ya bayana cewa a yanzu dai gwamnati na ciyar da dalibai miliyan 6,044,625 a makarantu 33,981 a jihohin da suka hada da Anambra, Enugu, Oyo, Osun, Ogun, Ebonyi, Zamfara, Delta, Abia, Benue, Plateau, Bauchi, Taraba, Kaduna, Akwa-Ibom, Cross River, Imo, Jigawa, Neja da Kano sannan a dalilin wannan shiri mutane 40,000 sun sami aikin yi.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta tsara shirin ciyar da yara ta hanyar da za ta iya tabbatar da ingancin abincin da ake ciyar da su.

” Sannan ma’aikatar kiwon lafiya ta shigo da shirin bada maganin tsutan ciki ga daliban aji daya zuwa shida a duk makarantun da suke cikin wannan shirin ciyar da dalibai.”

Share.

game da Author