A ranar Laraba ne gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abubakar ya nada sabbin kwamishinoni 19 a jihar.
Abubakar ya nada kwamishinonin ne bayan watanni shida da ya rusa majalisar zantarwar jihar.
Ya kuma yi kira a gare su da su yin aiki tukuru don ci gaban jihar da mutanen jihar, sannan ya kuma kwabe su da su guji duk aiyukkan cin hanci da rashawa cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.
Wadanda aka nada sun hada da:
1. Rifkatu Samson, kwamishinan Muhalli
2. Rukaiya Kewa, kwamishinan Al’amuran Mata da Ci gaban Yara
3. Haruna Mohammed, kwamishinan Shari’a
4. Umar Sade kwamishinan Yadda Labarai
5. Ibrahim Sale, kwamishinan Wasanni
6. Yakubu Kirfi, kwamishinan Aiyukan Noma
7. Mohammed Abubakar, kwamishinan ci gaban yankunan Karkara
8. Nasiru Giade, kwamishinan Harkokin Kasuwanci
9. Muhammadu Bashir, kwamishinan Wutan Lantarki, Kimiya da Fasaha
10. Umar Mohammed, kwamishinan gidaje da filaye
11. Umar Gazali, kwamishinan Harkokin Kasuwanci da Manyan Masana’antu
12. Garba Akuyum, kwamishinan Kudi
13. Ado Aska, kwamishinan Harkokin adini
14. Nasirudeen Mohammed, kwamishinan harkokin kananan hukumomi
15. Zuwaira Ibrahim,kwamishinan kiwon lafiya
16. Ibrahim Suleiman, kwamishinan Ruwa
17. Haruna Danwanka, kwamishinan Ilimi
18. Musa Baima, kwamishinan Ma’adanai
19. sannan mataimakin gwamnan Nuhu Gidado,zai shugabanci ma’aikatar aiyukkan da sufuri
Discussion about this post