Wata jami’ar kiwon lafiya Hellen Bulu ta yi kira ga mata da su daina yi wa jarirai wanka da ruwan zafi da zaran an haife su.
Ta fadi haka ne a taron wayar da kan mata mahimmancin yi wa ‘ya’yansu alluran rigakafi wanda aka yi a Abuja a makon jiya.
Bulu ta ce yi wa yara wanka da ruwan zafi tare da ja wa jariri hannaye da kafafu da akeyi lokacin da aka haihu na illata lafiyar jariri. ” Kuma hakan an fi yin sa ne a kasahen mu na Afrika.”
Tace hakan da ake yi kan iya sanadiyyar rayuwar jarirai.