Ganduje ya nemi duk makiyaya su koma jihar Kano

0

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya kira dukkan wani Bafulatani makiyayi da ke kasar nan, da ya tattara dabbobin sa ya yi hijira zuwa Kano.

Ganduje ya ce duk wani Bafulatani da ke fuskantar tsangwana a ko’ina ne a cikin kasar nan, to ya yi hijira zuwa jihar Kano akwai filaye isassu da za su yi kiwo ba tare da wata tsangwama ba.

Ganduje ya ce shi bai ga dalilin da zai sa a rika samun rikici da manoma da makiyaya ba, tunda Kano akwai filin kiwo wadatacce.

“Ina gayyatar kowane makiyayi da ke fadin kasar nan, ya dawo Kano saboda mu na da wadataccen fili da kowa zai yi kiwo ba tare da tsangwama ba.”

Gwamnan na Kano ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke kaddamar da shanu miliyan daya da sauran kananan dabbobi allurar rigakafi a Karamar Hukumar Garun Malam ranar Lahadi.

Wannan kashe-kashe da ake yi tsakanin makiyaya da manoma dai ya yi kamarin da wasu jihohi da suka hada Benue, Taraba da Ekiti har sun kafa dokar na kiwo a jihohin su.

Ganduje ya ce da wuya a ga Fulanin jihar Kano sun yi kaura su tafi kiwo wasu jihohi.

Sai ya ce Dajin Falgore kadai zai iya daukar miliyoyin shanu, kuma an tsara shi har da tsarin gina makarantu, asibitin jama’a da na dabbobi, kasuwanni, wuraren shakatawa da kayan more rayuwar karkara da za su samar wa makiyaya walwala da sukunin yin kiwo da kasuwanci.

Share.

game da Author