FYADE: Kotu ta daure wasu mazaje uku

0

Kotu dake Ado- Ekiti a jihar Ekiti ta yanke wa wasu mazaje uku hukuncin zaman a kurkuku saboda fyan da suka yi wa ‘yar shekara 14.

Dan sandan da ya shigar da karar Oriyomi Akinwale ya ce Samuel Farotimi dan shekara 27, Sunday Ajimoko mai shekaru 40 da Sunday Ilugbo mai shekara 30 sun hada kai ne suka yi wa wannan yarinya mai shekaru 14 fyade yayin da take dawo daga aike ranar 29 ga watan Janairu da misalin karfe tara na yamma a Ado-Ekiti.

Daga karshe alkalin kotun Dolapo Akosile ta yanke hunkuncin daure wadannan mazaje uku a kurkuku har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin da ake gurfanar da mutanen da suka aikata irin wannan laifi.

Za a ci gaba da sauraron karan ranar 14 ga watan Maris.

Share.

game da Author