Facebook zai taimaka wa INEC wajen wayar da kai a yi rajistar zabe

0

Babban dandalin sada zumunci na soshiyal midiya, wato Facebook, ya bayyana cewa a shirye ya ke da ya taimaka wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, wajen wayar da kan ‘yan Najeriya su yi rajistar zaben 2019.

INEC ta bayyana cewa wannan furuci ya fito ne daga bakin wata tawagar musamman daga kamfanin Facebook, karkashin jagorancin Daraktan Yada Labarai na Afrika, Ebele Okobi, yayin da su ka kai wa Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ziyara a hedikwatar INEC, a Abuja ranar Laraba.

Facebook, wanda matashi Mark Zuckerberg ya kafa cikin 2004, ya na da mabiyan shafin sama da bilyan daya a duniya, wadanda milyan 80 daga cikin su duk ‘yan Najeriya ne.

Okobi ta bayyana cewa sun yi nazarin cewa daga cikin ma su amfani da Facebook a Njeriya, mafi yawa sun fi tattauna batun zaben 2019 ne da kuma siyasa.

“Jama’a su na sa-ido kuma sun damu matuka dangane da irin yadda ake mulkin su, wadanda ke shugabantar su da kuma irin tafiyar gwanati. To ganin yadda jama’a ke shiga Facebook su na tattauna batutuwa na siyasa da mulki da dimokradiya, sai mu ka fito da wani tsari ko shiri domin mu gane yadda ake amfani da Facebook, ba wai lokacin zabuka kawai ba ma. Har ma yadda za a yi amfani da wannan hanya wajen wayar da kai dangane da zabe.”

Ta ce kamfanin na su ya bar kofa a bude domin ganin su bayar da gagarimar gudummawa wajen inganta harkokin zabe a Afrika, musammamn a Najeriya.

Farfesa Yakubu ya shaida musu cewa Hukumar Zabe ce ke da nauyin gudanar zabe a kasar nan, amma abin akwai kalubale sosai.

Daga nan sai ya gode wa Facebook dangane da yadda su ka kulle shafukan bogi na Facebook da kuma kasancewa INEC ta fi sauran hukumomin zaben kowace kasa mabiya a shafin ta na Facebook.

Yakubu y ace INEC za ta duba hanyoyin hadinn kai da Facebook a inganta hanyoyinn wayar da kai wajen tashi a himmatu a yanki rajisata da sauran su.

Share.

game da Author