Enugu za ta dauki sabbin Likitoci 28

0

Gwamnatin jihar Enugu ta sanar cewa za ta karo kwararrun likitoci 28 wa duk cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Finitin Ekochin ya sanar da haka da yake zantawa da kamfanin dillancin labarain Najeriya a Enugu ranar Juma’a.

” Gwamnati ta kammala shiri tsaf don ganin cewa kowace cibiyar kiwon lafiya na matakin farko a jihar ta sami likitoci akalla hudu.”

Daga karshe Ekochin ya ce likitocin na da damar zabar inda suke so a tura su.

Share.

game da Author