EL-RUFAI YA MAIDA MARTANI: Ruwa ne ya kare wa dan kada, Talakawan Kaduna na tare da ni kuma sun shai da aikin da muke yi – Inji El-Rufai

0

Bangaren jam’iyyar APC a Kaduna yau ta rubuta wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai wasikar gargadi, cewa yana yi wa jam’iyyar zagon kasa, da yayi wa jam’iyyar bayani cikin awowi 48 ko kuma jam’iyyar a jiha ta dau matakin gaggawa kan sa.

Sannan ta dakatar da mai ba gwamna El-Rufai shawara kan harkar siyasa, Uba Sani, da kwamishin kudin jihar.

Jim kadan bayan sun aika wa fadar gwamnanti wannan wasikar gargadi, sai El-Rufai ya mai da wa wannan bangare na APC shimfidaddiyar amsa.

A wasikar sa El-Rufai ya ce ya ji duk gadarar da Sanata Hunkuyi yayi cewa wai sai ya cire El-Rufai daga kujerar gwamnatin jihar Kaduna ya dora kan sa.

“ Abin da nake so Hunkuyi ya sani shine kada ya manta yadda yayi ta yi wa wadanda yake tare dasu yankan baya don ya zama gwamnan jihar Kaduna, amma hakan bai yiwu ba. Ya je ya kafa bangaren jam’iyyar APC a gidan sa wai ita ce jam’iyya. Ya sani cewa abin da yake so ba zai samu ba domin mutanen jihar Kaduna kai har da na garin sa Hunkuyi sun shaida abin da muke yi wa talakawa.

“ Ruwa ne ya kare wa dan kada, Hunkuyi na neman inda zai rabe ne kawai. Amma wannan jam’iyya za ta san yadda za tayi duk makarkashiyar da suke shirya mata.

Karanta labarin a harshen mu na turanci a nan: El-Rufai responds to APC faction’s query

Share.

game da Author