Hukumar EFCC ta gurfanar da Nanle Miracle Dariye, dan tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, a bisa tuhumomi shida da suka hada da wawure naira biliyan daya da rabi.
An gurfanar da shi ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, wadda ke karkashin Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu.
Mai gabatar da kara ya bayyana cewa Nanle Dariye ya karbi kudi zunzurutu har naira biliyan 1.5 a cikin 2013, wadanda aka tura masa a asusun ajiyar bankin mai sunan wani otal, kuma har yau bai maida kudin ba.
An bayyana wa mai shari’a cewa kudaden da aka tura masa sun zarce ka’idar naira milyan 10 kacal da dokar kasa ta amince a tura a irin wannan asusun ajiyar kudi.
Bugu da kari kuma an bayyana cewa shi kan sa otal din an yi masa rajista ne kawai da sunan wurin saukar baki, ba kamfanin kasuwanci ko zuwa jari ba, amma sai ga shi an zurara masa naira har biliyan 1.5.
Sunan otal din dai ‘Apartment le Paradis Limited’, kuma Nanle ne Babban Daraktan otal din.
An dai bayar da belin sa a kan sharadin cewa a ci gaba da tsare shi har sai an samu masu beli mutum biyu sun ajiye wa kotun naira miliyan 5, kuma su kasance mazauna Abuja ne.
Har ila yau, kowanen su sai ya gabatar da shaidar biyan haraji na shekarun 2015, 2016 da 2017.