Dubban magoya bayan jam’iyyar APC da suka kai akalla 2500 ne suka sanar da canza Sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP a Jihar Benuwai.
Masu canza Shekar duk sun fito daga garin Gboko na karamar hukumar Obadigbo sannan sun shaida cewa rashin Iya gudanar da mulki da jam’iyyar APC ke yi a kasa ne yasa suka yanke hukuncin komawa PDP.
” Gwamnatin APC ba su damu da mutanen Jihar ba. Sannan maganar rikicin fulani makiyaya da manoma a Jihar bai dada gwamnatin Najeriya da kasa ba, wanda haka yasa muka ga jam’iyyar PDP tafi dacewa da mu.