Dalilin da ya sa mu ka bijire wa sauya ranakun zabe – Sanata Abu Ibrahim

0

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Harkokin ‘Yan Sanda, Sanata Abu Ibrahim, ya bayyana cewa sun bijire wa yunkurin da majalisar tarayya ke yi domin sauya lokutan zabe, saboda babu wani dalilin da zai sa a sauya ranakun da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Kasa, INEC ta sa ranar gudanar da zaben.

A wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES, Abu Ibrahim, wanda Sanata ne daga jihar Katsina, ya nuna cewa ba tun yau aka fara neman sauya ranaku ba, amma da ya ke ana bin baudaddiyar hanya ce, shi ya sa yunkurin ba ya yin nasara.

Ya tunatar da cewa ko a zamanin Obasanjo, an wasu a Majalisar Tarayya sun nemi a rika gudanar da zabukan gaba daya a rana daya, amma ba a yi nasara ba.

Abu Ibrahim, ya ce idan za a tuna, kashi biyu bisa uku ne na majalisa su ka amince a rika yin zabukan duk a rana daya a cikin 2003, amma sai shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo ya ki sa wa dokar hannu.

“INEC ta je kotu a lokacin ta na kalubalantar yunkurin gudanar da zabukan a rana daya. A karshe Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin cewa harkar zabe ta hukumar zabe ce, don haka kada wadna ya kuskura ya yi wa INEC katsalandan.

Da aka tambaye shi batun kafa ‘yan sandan jihohi, Abu Ibrahim, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin ‘Yansanda, ya ce akwai matsala sosai a tattare da wannan tsari.

Ya tunatar cewa tun a cikin 1954 aka fara tunanin yin haka, har aka kafa Kwamitin Willink, wanda ya ce rashin alfanun kafa su ya rinjayi kafa su. Domin a cewa kwamitin, za a rika amfani da ‘yan sandan jihohi ana musguna wa kananan kabilu.

Don haka a yanzu kuma, sai Ibrahim ya ce bai kamata a yi amfani da ‘yan sandan jihohi a manyan al’amurra kamar gudanar da zabe ba.

Amma idan batun kama masu laifi ne da sauran kananan ayyukan inganta tsaron jama’a da dukiyoyin su, don jihar da za ta iya kafawa ta kafa, ai ba laifi ba ne.

Sanatan ya ce idan aka ce za a fara gudanar da zaben sanatoci da na mambobin majalisar tarayya, kamar yadda wasu ke so a sauya, to kusan kowa sai ya kashe makudan kudade wajen daukar ejan-ejan da sauran hidindimu.

Amma idan a loakaci daya aka yi su da na Shugaban Kasa, to kusan komai daga bangaren jam’iyya za a gudanar da shi, ita kuma gwamnatin tarayya ta bayar da jami’an tsaro.

Share.

game da Author