Dalilin da ya sa gwamnati ta rusa ofishin APCn Hunkuyi a Kaduna – KASUPDA

0

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa wasu daga cikin dalilan da ya sa suka rusa ofishin APC bangaren sanata Suleiman Hunkuyi wanda gidan sa ne na kan sa shine rashin biyan kudin harajin kasa.

Ma’aikatar raya birane na jihar KASUPDA, ta fadi a wata takarda da shugaban hukumar ya saka wa hannu, Ibrahim Husseini, cewa a ci gaba da kokarin gyara garin Kaduna da ma’aikatar sa ta ke yi, da samar da tsaro a jihar ne ya sa aka rusa wannan gida.

” Sannan kuma tun shekarar 2010, rabon da a biya kudin kasa na wannan gida.

” Ba tun yanzu ba ma’aikatar Sufeyo na jihar ta aika wa wannan gida takardun gargadi na rashin isassun takardun mallaka da rashin biyan kudaden harajin kasa. An tura wannan wasika ta akwatin aikawa da sako, an kai wa wannan gida takardar sanarwa hannu da hannu tun ba yanzu ba.” Inji KASUPDA.

KASUPDA ta ce wannan wuri za a amida shi wajen shakatawa na yara.

Share.

game da Author