Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da korar wasu manyan alkalai biyu, biyo bayan rahoton da Hukumar Sa-ido Kan Alkalai ta Kasa, NJC ta aika masa.
Alkalan sun hada da Babban Mai Shari’a Adeniyi Ademola, na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da kuma Babban Mai Shari’a O.O Tokode, wanda ke Babbar Kotun Tarayya ta Benin.
Wata takardar da kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya sa wa hannu, ta bayyana cewa an yi wa alkalan biyu ritayar tilas ce sakamakon dukkan su sun karya dokar kasa ta shekarar 1999, mai lamba 292 (1) (b).
Bayan wannan, an kuma umarci O.O Tokode da ya maida wa gwamnati dukkan albashi da kudaden alawus din da ya karaba tun daga ranar 2 Ga Disamba, 2015 har zuwa jiya Juma’a, ranar da aka tsige shi.
Hukumar NJC dai ta yanke shawarar aike wa Shugaba Muhammadu Buhari sunayen Ademola da Tokode ne a zaman da ta yi na ranar 2 Ga Disamba, 2017, saboda samun su da aka yi da harkalla, barankyankyama da cuwa-cuwa.
Discussion about this post