Dalilan da su ka sa Sanatoci sauya ranakun zaben 2019

0

Wasu mambobin Majalisar Dattawa sun bayyana wa PREMIUM TIMES a asirce cewa an yanke shawarar sauya ranakun da za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya ne saboda wasu darussa da aka koya a zabukan baya da kuma wani nazari da aka yi wa zaben 2019 mai zuwa.

Jadawalin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta fitar, ya nuna cewa za a yi zaben majalisar tarayya da na shugaban kasa a ranaku daya.

Sai dai kuma a wannan sauyin ranaku da majalisa ta yi, za a fara yin zaben majalisar wakilai da dattawa a rana daya, kafin zaben gwamnoni da na majalisar jihohi a ranaku daya su ma.

Sannan kuma, zaben shugaban kasa ne za a yi a ranar karshe kenan.

Wannan ne gyaran da suka yi wa dokar zabe ta sashen doka na 25.

Dama majalisar wakilai ta tarayya ce ta fara yin wannan gyaran, makonni kadan bayan INEC ta fitar jadawalin ranakun da za a gudanar da zaben.

Sai dai kuma da aka kawo gyaran dokar a majalisar dattawa domin tabbatarwa kuma a mika wa shugabn kasa, an nemi a kai ruwa rana tun a ranar Laraba da ta gabata.

Wasu sanatoci daga jam’iyyarc APC sun fice majalisar a fusace, su na masu zargin cewa an kulla makarkashiyar neman tadiye Buhari ne a zaben 2019, shi ya a ake kokarin a sauya ranakun zaben, har aka maida na shugaban kasa a karshe.

Amma wasu sanatoci biyu, wadanda suna a sahun gaba na sauya ranakun, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an sauya ranakun ne dalilin Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai kuma sanatocin sun nemi a sakaya sunayen su, domin kada fadar shugaban kasa da kuma uwar jam’iyya su yi musu bi-ta-da-kulli.

Dan majalisa ya bayyana wa PREMIUM TIMES asalin yadda aka nemi sauya ranakun zaben tun daga rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC.

” Mun yi canjin ne saboda rikicin da ya tirnike jam’iyyar APC ganin yadda mu ke da masaniyar cewa gwamnoni ba za su bari sanatoci da mambobin majalisar tarayya su sake tsayawa takara ba, wai za su maye gurbin su ne da na su ‘yan takarar da su ke so su tsaida.” Inji dan majalisar.

“Mun ga kusan kashi 70 ko ma kashi 80 bisa 100 na sanatoci da mambobin majalisar wakilai ta tarayya da ke karkashin jam’iyyar APC, na kokarin komawa wata jam’iyya. Don haka, magana a nan ita ce, idan su ka koma wata jam’iyya, to da wahala su tsaya zabe su yi nasara. Amma idan aka yi sauyin ranakun zaben, to duk inda mutum ya tsaya takara, za a iya zabar sa a kan cancantar sa.’’

“Ka ga dai wannan sabon tsari zai taimaka wa bangarorin mutane har uku. Na farko shi ne dan jam’iyyar APC wanda aka kuntatawa a cikin jam’iyyar sa, na biyu kuma zai taimaka wa wanda ya tsaya zabe a karkashin kananan jam’iyyu. Sai cikon na uku shi ne haka zai taimaka wa PDP.”

Dan majalisar ya ce don haka maimakon su tsaya su na fada da shugaban kasa, sai su ka ga gara kawai su tsaya su kare manufofin su na siyasa.

“Amma su wadanda ba su amince da wannan tsarin ba, sun fito su na cewa an yi shirin ne domin a tadiye shugaban kasa.

Su na cewa idan aka raba zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa da mambobi, to APC ba za ta fitar da kudi a ba ejan-ejan ba. Wai sai idan an hada zaben majalisa da na shugaban kasa ne sannan APC za ta bayar da kudin da za a dauki ejen-ejen.”

Shi kuwa dan majalisa na biyu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun yi haka ne domin su goge dalilin da ake cewa wai dukkan su sun ci zaben 2015 albarkacin Buhari.

Su na ganin wannan kamar wani cin fuska ne aka yi musu. Shi ya sa su ke so a fara yin na su zaben kafin na shugaban kasa, domin su nuna wa jama’a cewa su ma fa da bazar su, suke rawa, ba bazar Buhariyya ba.

Share.

game da Author