Dakarun Najeriya sun ceto dubban mutane da Boko Haram ta yi garkuwa da su

0

Rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa dakarun ta sun ceto mutanen da Boko Haram ta yi garkuwa da su har su 1,127 daga yankin Chadi.

Jagoran rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Onyema Nwachukwu ya sanar da haka a yau Talata inda ya kara da cewa sun sami nasarar kashe ‘yan Boko Haram 35 a arangamar da su kayi da su sannan sun kwato makamai da dama.

A ranar 26 ga watan faburairun 2018 dakarun sojin Najeriya da ke aiki a yankin arewa maso gabashin kasar nan wato ‘Operation Lafiya Dole’ da hadin guiwar dakarun sojin kasar Kamaru sun fatattaki Boko Haram inda suka sami nasarar kwato makamai 15 sannan suka kashe ‘yan Boko Haram 33 a kauyukan Kusha-Kucha, Surdewala, Alkanerik, Magdewerne da Mayen.

Bayan haka kuma sun lalata bama-bamai 4, sannan sun kona babura da kekune da dama. Sojojin sun ceto mutane 603 da Boko Haram tayi garkuwa da su inda yanzu suna garuruwan Bama da Pulka ana tanttance su kafin a mikasu ga ma’aikatan sansanonin ‘yan gudun hijira dake Barno.

Dakarun sun yi batakashi da Boko Haram a kayukan Bokko, Daushe da Gava inda suka sami nasarar kashe biyu daga cikin su sannan suka kwato bindiga daya, harsashai, jarkunan mai da mutane 194. Sannan kuma a haka dakarun sun ceto maza 3, mata 121 da yara 209 a kayukan Miyanti da Wudila da kuma makamai masu dimbin yawa a wasu maboyar Boko Haram bayan sun fatattake su.

Share.

game da Author