Wasu yara ‘yan makarantan firamare dake LEA II Kubwa, Abuja masu suna Nehemiah Yahaya da Yahaya Garba sun rasu yau bayan cin biskit a wani walima da suka je.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja Anjuguri Manzah, ya bayyana cewa ba su kama wanda ya ba yaran biskit din ba sai dai an rufe makarantar zuwa ranar litini 28 ga watan Faburairu.
Discussion about this post