Da alama bafulatanin gaske, wato ni, da jabu ne, wato Buhari, za mu gurza a 2019 – Sule Lamido

0

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya kaddamar da kamfen din sa na neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2019.

Sule dan jam’iyyar PDP ne, kuma tsohon gwamna, kuma tsohon minista.

Duka da cewa ya karya dokar hukumar zabe na fara gudanar da gangamin siyasa yanzu, da ya kamata sai wajen karshen shekarar nan ne shi dai ya kaddamar da tasa a garin Birnin Kudu, jihar Jigawa.

A wajen taron Sule ya ya ce duk da cewa Buhari bafulatani ne a asali, ba zai iya cewa komai da fulatanci ba wato fulfulfde.

Bambamci na da Buhari shine duk da ya taba yin gwamna a lokacin yana soja, bai tabuka komai ga mutane ba, sannan yayi ministan mai amma babu wanda ya san sa. “Ni kuwa da nayi minista kowa ya sanni a duniya.”

Ya zargi gwamnatin Buhari da nuna son kai kan yaki da cin hanci da rashawa, cewa mutane kamar su shugaban Kamfanin mai na kasa, Maikanti Baru, tsohon sakataren gwamnatin tarayya David Babachir, da Babagana Kingibe, duk shafaffu da mai ne a wannan gwamnati.

” Sun daure ni, sun kira ni barawo, amma abin da nake so in gaya musu shine duk da muzguna mini da suka yi, ba zai hani zama shugaban kasa ba a 2019. ”

A karshe ya bayyana wa daddazon magoya bayan sa a wajen taron irin wahalhalun da yasha a tsawon shekaru 40 da yake murza siyasa a kasar nan.

Share.

game da Author