Kwamishin kiwon lafiya na jihar Neja Mustapha Jibril ya sanar da cewa cutar sankarau ta bullo a jihar sannan mutane hudu sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar.
Jibril ya sanar da haka ne ranar Laraba da yake zantawa da manema labarai inda ya kara da cewa sun sami tabbacin cewa cutar ta bullo a kananan hukumomi biyu da ya hada da Magama da Katcha.
” Mun gwada mutane 31 daga wadannan kananan hukumoni inda muka gano cewa mutane tara ne suka kamu da cutar sannan hudu sun rasa rayukan su.”
A karshe Jibril ya ce za su hada hannu da ma’aikatar kiwon lafiya, kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, Asusun bada tallafi ga kananan yara na majalisa dinkin duniya UNICEF, kungiyoyi masu zaman kan su da sauran su domin shawo kan yaduwar cutar.
Discussion about this post