Yau Asabar ne Allah ya yi wa ‘yar Buhari, Hajiya Halima rasuwa.
Halima Dauda, ‘ya ce ga shugaba Buhari, kuma kanwar dan-uwan sa Mamman Daura, an yi jana’izar ta yau Asabar a Daura.
Marigayiya Halima ta rasu ta na da shekaru 56, sannan ta bar ‘ya’ya 10, cikin su akwai Mohammed Sabi’u Tunde.
Sai dai kuma kafin a yi jana’izar marigayiya Halima, sai da akayi jana’izar mai dakin babban wan shugaba Buhari, Alhaji Mamman da yamma Juma’a.
Jami’an gwamnati da gwamnonin kasar nan ne suka halarci jana’izan mamatan.