Cibiyar Binciken Labarai Da Bayanai, wato ‘ Premium Times Center For Investigative Journalim’ PTCIJ ta kirkiro sabbin shafuna a yanar gizo masu suna, ‘DUBAWA’ da ‘UDEME’ don bankado harkalla da sanin sahihancin labarai da irin ayyukan da gwamnati take yi ko ya kamata tayi a garuruwan ku da irin wadanda ‘yan majalisun ku ya kamata su yi muku.
DUBAWA: www.dubawa.org
Dubawa shafi ne da aka kirkiro don ba mutane damar sanin sahihancin bayanai da za su karanta a shafunan jaridu da wadanda gwamnati ke fadi da ga hukumomin ta ne ko ma’aikatun ta.
Dubawa zai samar maka da hanyoyin iya tantance gaskiyar labarin da za ka iya kicibus da shi ko ta kafofin yada labarai ko kuma ta bayanai daga jami’an gwamnati.
Sanin kowa ne cewa yanzu ana fama yayyada rahotannin karerayi musamman a shafunan sadarwa da kafafen yada labarai da wasu da yawa kan kafa hujja da su bayan hakan basu da asali. Gane wani labari, ko rahoto ne mai gaskiya kan zama abin wahala musamman a halin da ake ciki yanzu.
Dubawa, zai dubo maka sannan ya fede maka biri da kai har wutsiya game da duk bayanan da kake neman sani da ingancin sa. Kama bayanan gwamnati ne, ayyukan ma’aikatun gwamnati, da kudaden da ake cewa an kashe a ayyuka da sauran su.
Za a bi shafin dubawa ne ta www.dubawa.org
UDEME: www.udeme.ng
Bayan haka, Cibiyar PTCIJ, ta kirkiro shafin Udeme wanda shima zai yi aiki ne wajen dada wayar wa mutane kai da tantance gaskiyar al’amura da bayanai.
Shafin Udeme zai baka bayanai ne dalla dalla game da irin ayyukan da ya kamata ayi a gundumomi, yankuna, kauyuka, da garuruwan ku kamar yadda gwamnati ta samar a kasafin kudin kasa.
Udeme zai baka damar sanin wani aiki ne Dan majalisar da kuka zaba ya kamata ya yayi a mazabun ku.
Udeme zai wayar maka da kai game da alkawuran da gwamnati ta dauka musamman wandanda suka shafi ababen more rayuwa da ya kamata a samar muku a garuruwan ku.
Sannan zai baka damar Iya bin diddigin ayyukan da ya kamata ka sani ko ana yi ko ba ayi a garin ka.
Za a bi shafin Udeme a: www.udeme.ng