A yau Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da makarantar nakasassu da gwamnatin jihar Nassarawa ta gina.
Buhari ya ce an gina makarantar wanda babu irinta a jihar domin nakasassu su sami ilimin boko daga firamare zuwa jami’a.
Ya ce hakan na nuna cewa gwamnatin sa na sane da nakasassu.
” Bayan kaddamar da wannan makaranta ya kuma kaddamar da cibiyar kiwon lafiya da sabuwar kasuwa.”
Buhari ya ce za a fara tsarin kiwon lafiya mai suna ‘Community Health Influencer Promoters and Services, CHIPS’ a jihar domin samar da ingantacciyar kiwon lafiya a saukake wa mazaunan karkara da talakawa a duk fadin kasar nan.
Daga karshe gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makura ya mika godiyar sa na musamman ga shugaban kasa sannan ya ce gina wannan makaranta zai taimaka wajen inganta rayuwar nakasassu ba a jihar ba kawai har da kasa Najeriya.