Buhari ya dawo da shugaban hukumar NHIS, Usman Yusuf

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo da shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa Usman Yusuf aikin sa yau.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya tabbatar wa PREMIUM TIMES dawowar shugaban hukumar NHIS din.

Ko da yake fadra shugbanan kasa bata bada wani cikakken bayani ba kan dawowa da Usman Yususf aikin sa umarnin dai ya fito daga fadar ne.

Idan ba a manta ba, da yammacin Alhamis din 6 ga watan Yulin 2017 ne ministan lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar bada inshorar kiwon lafiya ta Kasa ‘NHIS’ Usman Yusuf daga aiki.

Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewale ne ya sanya hannu a takardar dakatarwar.

Ana tuhumar Usman Yusuf da yin amfani da wasu kudade da ya kai naira Miliya 200 don gudanar da tirenin ga wasu ma’aikatan hukumar da kuma rashin jituwa dake tsakanin sa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewale.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce wasu daga cikin dalilan da ya sa ya dakatar da shugaban hukumar inshorar lafiya lafiya ta kasa NHIS Usman Yusuf shine don korafe-korafen da ake tayi kan sa na sama da fadi da yayi da wasu kudaden ma’aikatan da kuma zargi da akeyi masa na aikata wasu laifuka da ya saba wa dokar ma’aikatar.

Minista Isaac Adewole ya ce ya dakatar da Usman Yusuf na tsawon watanni uku ne saboda a sami damar gudanar da bincike akan zargin da akeyi a kansa.

Ga bayanan da ya iske mu zuwa yanzu, Shugaban Buhari ya umurci Yusuf Usman da ya koma aikin sa sannan su koma su daidaita kan su domin ci gaban ayyukan ma’aikatar.

Share.

game da Author