Buhari na ganawa da tsoffin shugabannin Najeriya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya na ganawa da tsoffin shugabannin kasar nan a yau Alhamis. Taron dai na gudana ne da karfe 11 na rana, wato yanzu haka ana tsakiyar ganawar.

Wannan shi ne karo na uku ga Buhari ya gana da shugabannin tun bayan hawan sa mulki cikin 2019.

Wannan zaman majalisar na tsoffin shugabannin kasar nan, su na a matsayin mambobin majalisar ce da ke ba shugaban kasa shawara.

Wasu daga cikin irin shawarwarin da sukan bayar sun hada da batun kidayar jama’ar kasa, batun yi wa wani mai laifi afuwa, bayar da lambobin yabo da kuma batun nada mambobin hukumar gudanarwar INEC da nada shugaban hukumar.

Mambobin wannan majalisa dai baya ga shugaban kasa mai ci kan mulki, akwai tsoffin shugabannin kasa, akwai kuma mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa da ta wakilai da kuma gwamnonin kasar nan 36, sai kuma ministan shari’a.

Tsoffin shugabannin da ake sa ran su na can ana gudanar da taron tare da su, sun hada da Shehu Shagari, Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da Ibrahim Babangida.

Sauran sun hada da Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar da Ernest Shonekan.

Share.

game da Author