A yau Asabar ne Boko Haram suka saki wasu ‘Yan sanda mata 10 da sukai garkuwa dasu da malaman jami’ar Maiduguri uku dake hannun su.
Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya sanar cewa hakan yayi wu ne bayan jerin tattaunawa da hukumomin Najeriya suka rika yi da ‘yan Boko Haram tare da hadin guiwar kungiyar agaji ta Red Cross.
Boko Haram tayi garkuwa da malama Jami’ar Maiduguri ne a lokacin da suke aikin nemo danyen mai a dajin Sambisa, sannan su kuma matan ‘yan sandan na kan hanyar su ne na zuwa Damboa, kusa da Maiduguri.