Kungiyar Tranparency International, ta lissafa wasu maka-makan gidaje guda biyu da ake kyautata zargin mallakar Shugaban Majalisar Dattawa ne, Sanata Bukola Saraki, domin a bincike su a karkashin sabuwar dokar Birtaniya.
An dai kafa wannan sabuwar dokar binciken kadarorin da ba a tantance masu mallakar su ba, kuma dokar ta fara aiki tun a ranar 31 Ga Janairu, 2018.
Kungiyar TI ta ce ragistar mallakar gidaje da filaye ta nuna cewa gidaje biyu masu lamba 7 da 8, da ke kan Titin Whittaker, a unguwar Belgravia, cikin Landon, mallakar wani kamfani ne, mai suna Landfield International Development Limited da kuma Renocon Property Development Limited.
To a wani kiyasin kudin gidajen biyu da kamfanin kiyasin kadarori na Zoopla ya gudanar, ya nuna gidajen biyu sun kai fam milyan 15.
Wani bincike da PREMIUM TIMES ta gudanar, ya nuna cewa wadannan kamfanoni karkashinn kulawar Sanata Toyin Saraki ce, matar Bukola Saraki da kuma daya daga cikin hadiman Saraki.
Har zuwa lokacin da ake rubuta labarin nan, wadannan kamfanoni biyu da aka sake bankadowa, ba su cikin kadarorin da Saraki ya yi rantsuwar ya mallaka.
A daya bangaren kuma, Saraki na ci gaba da fuskantar wata sabuwar tuhumar laifin mallakar wasu kadarorin da bai sa su a cikin jerin dukiyar da ya mallaka da bai gabatar da su ga hukuma su ba.
Can baya kotun CCT ta salami karar da aka dade ana yi kan sa. Sai yanzu kuma aka sake gurfanar da shi a CCT din a kan wata harkallar daban.
Wannan ya zame wa Shugaban Majalisar Dattawa gaba damisa baya siyaki kenan.